Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Nasarawa Daniel Iya ya ce suna zaton wani mutum daya a jihar ya kamu da cutar ‘Monkey Pox’.
Daniel ya fadi haka ne da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai a garin Lafiya.
Ya ce an aika da jinin sa don a gwada a Legas.
” Yanzu Haka muna sauraron dawowar sakamakon gwajin ne.”
Ya yi kira ga mutanen jihar da sarakunan gargajiya da su taimakawa gwamnati wajen ganin an wayar da kan mutane game da ingancin tsaftace muhalli da gaggauta zuwa asibiti da zaran ba’a jin dadi a jiki.
Source: Premium Hausa
Title :
Ana Zaton Wani Yakamu Da Cutar Money Pox A Nasarawa
Description : Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Nasarawa Daniel Iya ya ce suna zaton wani mutum daya a jihar ya kamu da cutar ‘Monkey Pox’. Daniel ya fad...
Rating :
5