Mahukunta a Spaniya sun zargi dan kwallon Real Madrid Marcelo da kin biyan haraji da ya kai kudi fam 436,000.
Masu shigar da kara sun alakanta rashin bin ka'ida da dan kwallon ya yi ta hanyar bude kamfani a waje da yake kula da kudin da yake samu ta fuskar tallace-tallace.
Har yanzu dai Marcelo mai shekara 29 dan kwallon tawagar Brazil, bai ce komai ba dangane da zargin da ake masa.
Shi ne dan wasa na baya-bayan nan da mahukuntan Spaniya ke zargi da kaucewa biyan haraji, bayan Messi da Neymar da Ronaldo.
Lamarin ya faro ne tun daga shekarar 2013.
Source: BBC Hausa
Title :
Ana Zargin Marcelo Da Kin Biyan Haraji
Description : Mahukunta a Spaniya sun zargi dan kwallon Real Madrid Marcelo da kin biyan haraji da ya kai kudi fam 436,000. Masu shigar da kara sun alaka...
Rating :
5