Wani dan kasar Scotland da ke fuskantar daurin shekara uku a gidan yari a Dubai, ya bayana a gaban kotu, bisa tuhumar taba kugun wani namiji da hannunsa a wani wurin shakatawa.
Jamie Harron daga Stirling, ya bayana a gaban kotu ne a ranar Lahadi bayan ya gaza halartar zaman kotu na farko da aka yi a birnin.
Mutumin mai shekara 27, an kama shi ne bisa zargin rashin kamun kai sakamakon lamarin da ya faru a wani wurin shakatawa na Rock Bottom da ke Dubai a ranar 15 ga watan Yuli.
Duk da fargabar da aka nuna a kan cewa za a sake kama shi, an sako Mr Harron din, amma an fada masa cewa ya ci gaba da zama a garin, har zuwa lokacin da kotu za ta saurari karar.
Mutumin wanda mai gyaran wutar lantarkin ne da ke aiki a Afghanistan, ya kawo ziyarar yini biyu ne a Hadaddiyar Daular Larabawa lokacin da lamarin ya faru.
Ya yi ikirarin cewa ya yi kokarin ganin cewa lemun da yake sha a kofin gilashi, bai zuba a jikin mutane ba, a kulob din da ya cika makil da jama'a, kuma ya mika hanunsa ne lokacin da ya taba kugun wani bisa kuskure domin hana lemun zuba a jikinsa.
Rahotani sun ce ya yi kwanaki biyar a gidan yarin Al Barsha, kafin aka ba da belinsa, sai dai an kwace masa fasfo dinsa.
Mai magana da yawun kungiyar agaji ta "Detained in Dubai", da ke wakilatar Mr Harron, ta shaidawa BBC cewa ta rika tsammanin za a sake kama shi a ranar Lahadi, saboda gazawarsa na rashin bayyana a gaban kotu.
Ta bayyana farin cikinta a kan sakin da aka yi masa. Sai dai kuma zai sake gurfana a gaban kotu, kan tuhumar da ake yi masa na rashin kamun kai da kuma shan barasa.
Kamen na zuwa ne bayan wani dan Edingurgh da aka tsare a Dubai, bayan yunkurin sauya fam 20 na bogi da ya yi.
William Barclay, daga Edingburg ya koma gida a ranar Juma'a bayan da ya shafe kwana uku a Dubai yana tsare lokacin da suka je hutu da iyalinsa.
Source: BBC Hausa
Title :
Ana Tuhumar Wani Dan Scotland Da Taba Kugun Namiji A Dubai
Description : Wani dan kasar Scotland da ke fuskantar daurin shekara uku a gidan yari a Dubai, ya bayana a gaban kotu, bisa tuhumar taba kugun wani namiji...
Rating :
5