A ranar Litinin ne za a fara wani taro na yini uku a Dakar babban birnin kasar Senegal, da nufin bullo da wasu sharudda na hana auren wuri.
Taron zai hada matan shugabannin kasashen nahiyar da ministoci da shugabannin addini da kuma sarakunan gargajiya na gwamnatocin kasashen yammaci da tsakiyar Afrika da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Save the children mai kare hakkin yara, da kungiyoyin kare hakkin bil adama ne suka hada hannu don 'yanto kananan yaran da ake yi wa auren wuri.
An dai shirya taron ne da nufin fahimtar da al'ummomin nahiyar Afirka a kan illolin da ke tattare da auren wuri.
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, da kungiyar Save The Children, sun nuna bukatar da ke akwai na daina aurar da 'ya'ya mata da wuri.
Kwararru sun ce duk da kokarin da ake yi na hana auren wuri, har yanzu akwai kasashe shida daga cikin 10 da kurarsu ta yi kuka wajen aurar da 'ya'ya mata da wuri ciki har da Jamhuriyar Nijar, inda ake aurar da yara wadanda ba su kai shekara 18 ba uku a cikin hudu.
Masana na ganin cewa, auren wurin na shafar karatu da lafiyar yaran, don haka ya kamata a karfafa wa yaran gwiwa su yi karatu.
Source:BBC Hausa
Title :
Ana Taron Hana Auren Wuri A Afrika
Description : A ranar Litinin ne za a fara wani taro na yini uku a Dakar babban birnin kasar Senegal, da nufin bullo da wasu sharudda na hana auren wuri. ...
Rating :
5