Hukumar lafiya ta duniya ta nada shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, a matsayin farin jakada.
Sabon babban daraktan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ne ya sanar da nadin a wajen wani taro da aka yi a kan cutukan da basa yaduwa a Uruguay.
Nadin shugaban kasar ta Zimbabwe mai kimanini shekaru 93 a duniya zai zowa wasu daga cikin kasashe mambobin kungiyar da ma kungiyoyin agaji da matukar mamaki.
Mukamin farin jakada, mukami ne na mutumin da ya taka wata muhimmiyar rawa,to amma bayar da mukamin ga mutumin da ake sukar gwamnatinsa akan rugujewar tsarin kula da lafiya da kuma gagarumin cin zarafin bil adama, ba abu ne da zai yi tagomashi ba.
Sabon babban daraktan ya yaba wa shugaban na Zimbabwe bisa kokarinsa wajen kula da lafiyar al'umma, wanda hakan ne ya sa ya bashi wannan matsayi na farin jakada.
Sabon daraktan wato Dr Tedros, shi ne dan Afrika na farko da ya taba rike wannan babban matsayi,an kuma zabe shi ne a kan alkawarin cewa zai kawo sauyi a hukumar da kuma shawo kan yadda wasu ke jin hukumar na sanya siyasa cikin al'amuranta.
Wannan mataki na sabon daraktan zai sanya shakku a zukatan wasu akan yanayin shugabancinsa da ma ayyukansa
Source: BBC Hausa
Title :
Ana Mamakin Sabon Mukamin Da Aka Bawa Mugabe
Description : Hukumar lafiya ta duniya ta nada shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, a matsayin farin jakada. Sabon babban daraktan hukumar Tedros Adhan...
Rating :
5