Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano, ta ce jami'anta sun kebe wani mutum da aka ba da rahoton ya kamu da cutar kyandar birrai a jihar.
A ranar Alhamis ne dai aka fara rade-radin an samu wani mutum da ya kamu da cutar, bayan tun da farko da gwamnati ta ce wani shi ma da ake zargin ya kamu, ba cutar ce ta harbe shi ba.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Kabir Abubakar Getso, ya shaida wa BBC cewa, an samu mutum guda da ake zargin ya kamu da cutar a karamar hukumar Bebeji.
Kuma tuni aka dauke shi aka kai shi cibiyar da aka ware ta musammam don kula da wadanda suka kamu da irin wannan cuta ko makamanciyarta, in ji shi.
Dr Kabir Abubakar Getso, ya ce yanzu haka an fara yi wa wannan mutum gwaje-gwaje da kuma gudanar da cikakken bincike, don gano kowacce irin cuta ce.
Ya ce zuwa yanzu ba a tabbatar da ko kyandar birrai ba ce, sai abin da bincike ya gano tukunna.
Kwamishinan ya ce, ko a makon da ya gabata, an kawo musu wani da ake zargi ya kamu da cutar saboda kurajen da suka fito a jikinsa sun yi kama da na mai cutar.
Ya ce sai dai ko da a gwada sai aka gano ba ita ba ce.
Don haka ya ce yanzu bincike ne kadai zai tabbatar da ko cutar ce ta kama mutumin da ake zargi ko ba ita ba ce.
Ita wannan cutar dai ta samo asali ne daga jikin biri da sauran dabbobi kamar su bera da kurege da kuma barewa.
Source: BBC Hausa
Title :
Ana Bincike Ko Kyandar Biri Taje Kano
Description : Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano, ta ce jami'anta sun kebe wani mutum da aka ba da rahoton ya kamu da cutar kyandar birrai a jihar. ...
Rating :
5