An raba wasu 'yan biyu da aka haifa a hade a wurin cibiya a wani kauye me nisan gaske, a jamhuriyar Dimukradiyar Congo, bayan da suka shafe sa'oi 15 kan babur domin a yi masu aikin tiyata. An dai wuce da su Kinshasa babban birnin kasar, inda wasu likitoci suka yi masu aiki. Jariran mata masu suna Anick da Destin zasu koma kauyensu nanda makwanni 3 masu zuwa.
A Watan Augusta ne aka haifesu , suna da makwanni 37 kuma sun hade a wurin cibiya.Likitoci sun ji mamakin cewa mahaifiyarsu ta haihu ne a gida a kauyen Muzombo da ke yammacin kasar. Iyayen jariran, Claudine Mukhena da Zaiko Munzadi suka kai su wani asibiti dake kusa da kauyensu.
Sai dai rashin kayan aiki da kuma kwarewar ma'aikata ya sa likitocin sun wuce da su zuwa asibitin Kinshasha mai nisan mile 300.
Dr Junior Mudji da ke kula da jariran a asibitin Vanga Evangelican ya ce yana farinciki. Ya ce ba kasafai ake samun jarirai 'yan biyu yan makwanni talatin da bakwai ba, da aka haifa a hade a gida .
Ya ce zasu cigaba da zama a asibiti har na tsawon makwanni uku domin a tabattar komai na tafiya dai-dai.
Dr Mudji ya yi ammanar cewa wannan shi ne karon farko da aka raba yan biyu da aka haifa a hade a jamhuriyar dimukradiyar Congo
Source: BBC Hausa
Title :
An Raba Yan Biyun Da Aka Haifa A Hade
Description : An raba wasu 'yan biyu da aka haifa a hade a wurin cibiya a wani kauye me nisan gaske, a jamhuriyar Dimukradiyar Congo, bayan da suka sh...
Rating :
5