Gwamnatin Masar ta ce wani artabu tsakanin jami'an tsaronta da wasu 'yan ta-da-kayar-baya ya yi sanadin mutuwar akalla 'yan sanda 53 a yankin Saharar Kudancin kasar.
Haka zalika, an kashe su ma 'yan ta-da-kayar-baya 15.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce 'yan ta-da-kayar-baya sun bude wuta kan jami'an tsaron ne lokacin da suka kai wa maboyarsu samame a kusa da dausayin Bahariya.
Masar na fama da ayyukan 'yan ta-da-kayar-baya da ke tattare a yankin Sinai, akasari daga wasu manyan kungiyoyi guda masu alaka da ISIS.
Hare-haren 'yan ta-da-kayar-bayan dai ya yi sanadin mutuwar dakarun tsaron kasar da dama tun cikin shekara ta 2013.
Rahotanni sun ce an yi wa jami'an tsaro kwanton bauna ne, inda 'yan tada-kayar-baya suka far wa motocinsu da bindigogin roka.
Wata majiyar tsaro ta ce 'yan ta-da-kayar-bayan sun fi sanin yankin ciki da bai, kuma kwamandan jami'an tsaron ya gaza kiran a kai masa dauki.
Wani rahoto ya ce 'yan ta-da-kayar-bayan sun fito ne daga wata kungiya da ake kira Hasm, wadda ta saba far wa dakarun tsaro a baya.
Source: BBC Hausa
Title :
An kashe Yan Sandan Masar 53 A Wani Kwanton Bauna
Description : Gwamnatin Masar ta ce wani artabu tsakanin jami'an tsaronta da wasu 'yan ta-da-kayar-baya ya yi sanadin mutuwar akalla 'yan sand...
Rating :
5