Akalla sojojin jamhuriyar Nijar 12 ne suka rasa rayukansu lokacin da wadansu mahara suka kai musu hari a kan iyakar kasar da Mali ranar Asabar.
Maharan sun kai harin ne a cikin motocin akori kura da kuma kan babura a wani sansanin sojojin Nijar da ke iyakarta da Mali daga yammaci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tabbatar.
"Dakaru 12 ne suka mutu a wani sabon hari. Mun kaddamar da bincike game da harin a yankin Tillaberi," in ji Ministan Yada Labaran Nijar Mohamed Bazou.
Maharan sun fito ne daga kasar Mali, inda suka isa wani gari mai suna, Ayorou (mai nisan kilomita 40 daga kan iyaka), kamar hukumomin kasar suka bayyana.
A farkon watan nan ne wadansu mahara daga kasar Mali suka yi wa dakarun Nijar da na Amurka kwanton-bauna a garin Tongo-Tongo da ke arewacin jihar Tillabery, inda suka kashe sojin Amurka hudu da kuma na Nijar biyar.
Source: BBC Hausa
Title :
An Hallaka Sojojin Nijar 13 A Kan Iyakarta Da Mali
Description : Akalla sojojin jamhuriyar Nijar 12 ne suka rasa rayukansu lokacin da wadansu mahara suka kai musu hari a kan iyakar kasar da Mali ranar Asab...
Rating :
5