Gwamnatin Najeriya ta bukaci likitocin kasar da su yi taka tsantsan wajen tura majinyata zuwa asibitoci da ke kasashen waje.
Hakan ya biyo bayan shawarar ofishin masu gabatar da kara a Masar na bayyana sunayen wasu asibitoci hudu da ke a Alkahira, a wata shari'a ta mutane 41 da ake zargi da fataucin kodar jama'a.
Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ce ta fitar da wannan gargadi a wata sanarwa da ta aike wa shugaban kungiyar likitocin kasar, inda aka bayyana sunayen asibitocin.
Asibitocin sun hada da asibitin Dar-al Shafa a Helwan na birnin Al-Kahira da asibitin Al-Bashar Specialist a Faisal na birnin Giza, da cibiyar lafiya ta Al-Amal da ke Giza da kuma asibitin Dar ibn Al-Nafis a Giza.
A sanarwar da ya sanya wa hannu, ministan lafiya na Najeriya Farfesa Isaac Adewole, ya bukaci 'yan kasar da su yi taka tsantsan sosai wajen zabar asibitin da za su dinga zuwa a kasashen waje don gudun samun kansu cikin tashin hankali.
Rahotanni na cewa daga cikin mutanen da aka sace wa koda a Masar har da 'yan Najeriya da dama, kuma wadanda suka sace musu din na cikin wadanda aka gurfanar a gaban kotu.
Hakan ce ma tasa gwamnatin Najeriyar fitar da wannan gargadi ga 'yan kasar da su san irin asibitocin da za su dinga zuwa a kasashen waje.
Dubban 'yan Najeriya na tafiya kasashen waje duk shekara domin zuwa asibiti saboda rashiningantaccen tsarin lafiya a kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
An Gargadi 'Yan Nijeriya Kan Zuwa Asibitocin Turai
Description : Gwamnatin Najeriya ta bukaci likitocin kasar da su yi taka tsantsan wajen tura majinyata zuwa asibitoci da ke kasashen waje. Hakan ya biyo ...
Rating :
5