Kasar Amurka za ta taimakawa bangaren shari'ar Najeriya a kan batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka ya aike wa BBC, ta ce kasar za ta ba Najeriya kwafin wani littafi da ya kunshi yadda kotuna za su rika yanke hukunci kan shari'un da suka shafi cin hanci da rashawa.
Gwamnatin Najeriya dai ta yi alkawarin magance matsalar cin hanci da rashawa, amma tsaikon da ake samu a kotuna na yi wa hakan tarnaki.
Ko a baya ma, sai da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci wani taro a kan yadda za a inganta bangaren shariar kasar domin shirin gwamnatinsa na yaki da cin hanci da rashawa ya yi tasiri.
Wasu masu sharhi sun ce akwai bukatar ganin cewa an inganta kotunan kasar ta yadda za su dinga yanke hukunci cikin sauri da kuma adalci.
Source: BBC Hausa
Title :
Amurka Zata Taimakawa Kotunan Nigeria
Description : Kasar Amurka za ta taimakawa bangaren shari'ar Najeriya a kan batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa. Wata sanarwa da ofishin jak...
Rating :
5