Matar tsohon gwamnan jihar Gombe, Hajiya Yalwa Danjuma Goje, ta rasu bayan fama da rashin lafiya.
Hajiya Yalwa ta rasu ne a ranar Litinin da safe a kasar Amurka bayan ta sha fama da doguwar jinya da ba a bayyana ba.
Wata majiya mai karfi daga makunsantan marigayiyar ta tabbatar wa BBC cewa marigayiyar ta fara jinya ne a Indiya kafin daga bisani a mayar da ita Amurka inda ta rasu.
Hajiya Yalwa ta mutu ne tana da shekara 55, ta kuma bar 'ya'ya da jikoki da dama.
Hajiya Yalwa dai ita ce uwargidan tsohon gwamnan Gomben wanda a yanzu sanata ne a majalisar dattawa ta Najeriya.
Source: BBC Hausa
Title :
Allah Yayi Rasuwa Wa Matar Danjuma Goje
Description : Matar tsohon gwamnan jihar Gombe, Hajiya Yalwa Danjuma Goje, ta rasu bayan fama da rashin lafiya. Hajiya Yalwa ta rasu ne a ranar Litinin d...
Rating :
5