Shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont ya ce yankin dake cikin kasar Spaniya ya dauki hanyar kafa kasa mai cin gashin kanta bayan wani zaben raba gardama da ke cike da takardama.
Ya ce wannan ya bude kofa ga yankin ya yi shelar kafa kasar ba tare da izinin Spaniya ba.
Jami'an yankin sun ce kashi 90 cikin 100 na masu kada kuri'a sun zabi ballewa daga Spaniya, a zaben da aka gudanar ranar Lahadi. Kashi 42.3 cikin 100 na wadanda suka cancanci su kada kuri'ar ne suka sami yin haka.
Kotun kolin Spaniya ta riga ta haramta wannan zaben kuma daruruwan mutane sun sami raunuka a yayin da 'yan sanda suka yi amfani da karfi domin hana gudanar da zaben.
Jami'an na 'yan sanda sun rika kwace akwatunan zabe da kuri'u a rumfunan zaben.
"Daga wannan rana ta ishara da gwagwarmaya, al'ummar Catalonia sun zabar wa kansu damar kafa kasa mai cin gashin kanta wacce zata kasance jamhuriya ce," inji Mista Puigdemont a wata ganawa ta talabijin da yayi tare da wasu manyan jami'an gwamnatin yankin.
Ya kara da cewa "Gwamnatina zata mika sakamakon wannan zaben ga majalisar Catalonia domin ta rattaba wannan yunkuri na jama'armu."
Ya kuma ce a dalilin wannan zaben, tilas Tarayyar ta daina kau da kai dangane da yunkurin kafa kasar ta Catalonia.
An kara tsakanin jami'an tsaro da masu zabe
Gwamnatin yankin ta ce fiye da mutum 800 ne suka sami rauni a sanadiyyar karawa da jami'an 'tsaro a fadin yankin.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Spaniya ta ce 'yan sanda 12 sun sami rauni kuma an kam mutum uku. Ta kuma ce an rufe rumfunan zabe 92.
Source: BBC Hausa
Title :
Al'ummar Catalonia Sun Zabi Ballewa Daga Spain
Description : Shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont ya ce yankin dake cikin kasar Spaniya ya dauki hanyar kafa kasa mai cin gashin kanta bayan wani ...
Rating :
5