Matar shugaban kasar Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta yi tir da halin da bangaren lafiya na kasar ke ciki, kan yadda abubuwa ke kara tabarbarewa.
Hajiya Aisha ta ce abin takaici ne yadda idan aka duba halin da asibitin fadar shugaban kasa ke ciki, balle kuma a zo maganar sauran asibitocin kasar da ke jihohi ko karkara.
Ta bayyana hakan ne a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na wata hukumar kula da lafiyar mata da yara, wanda aka gudanar a asibitin da ke cikin fadar shugaban kasar.
Sai dai wannan bayani nata zai bai wa wasu 'yan kasar da dama matukar mamaki, ganin cewa wannan al'amari yana faruwa ne karkashin shugabancin mijinta, wanda ya karbi ragamar tafiyar da kasar fiye da shekara biyu da suka gabata.
Ta ce: "Na ji matukar dadi da nake wannan maganar a lokacin da shugaban asibitin fadar Dr. Hussain Munir yake nan, kowa ya san cewa wata shida da suka gabata mijina ba shi da isasshiyar lafiya, amma yanzu mun gode Allah ya samu sauki."
"Makonni kadan da suka gabata, na yi fama da rashin lafiya, sai likitocin asibitin fadar shugaban kasa suka shawarce ni cewa na hau jirgin farko zuwa London, amma sai na ki."
"Na ce musu dole ne a duba ni a gida Najeriya, saboda akwai kudin da aka ware musamman don kula da asibitin," in ji ta.
Hajiya Aisha ta kara da cewa: "Idan dai har shugaban kasa zai shafe watanni da dama a wani asibiti a kasar waje, to za a yi mamakin halin da talakan kasar kuma ke ciki wanda ba shi da gata."
"To idan har kudin da aka ware don kula da sibitin ya kai miliyan 100, za mu so mu san ta yaya aka kashe kudin. Rannan da nasa a tambaya ko suna da injin daukar hoton kashi sai suka ce ba ya aiki, ba su san cewa ni ce nake son zuwa a duba ni ba."
Uwargidan shugaban kasar ta kara da cewa hakan ne ya sa ta tafi wani asibitin kudi mallakin 'yan kasar waje don a duba ta.
A kan haka ne ta yi kira da cewa ya zama wajibi a yi abin da ya dace don magance wannan matsala.
"Idan har abu irin wannan zai faru da ni, to lallai ba na bukatar tambayar matan gwamnoni abin da ke faruwa a jihohinsu. Nan Abuja ce inda fadar shugaban kasa take.
"Duk da cewa na ji wani a jawabinsa ya ce Najeriya daga cikin kasashen da take da tsari mai kyau, lallai na yarda, amma matsalarmu ita ce jajircewa don ganin an aiwatar da abu."
A makon da ya gabata ne 'yar shugaban kasa Zahra Buhari ta caccaki asibitin fadar shugaban kasar a shafinta na Twitter, inda tuni wasu 'yan Najeriya suka fara ganin kamar Hajiya Aisha na goyon bayan abin da 'yarta ta fada ne.
kasafin kudin da aka ware na 2017 ga asibitin fadar shugaban kasa dai, wanda kuma majalisar dattawa ta amince da shi ya fi naira miliyan 330,000.
Source: BBC Hausa
Title :
Aisha Buhari Tayi Tir Da Asibitin Fadar Shugaban Kasa
Description : Matar shugaban kasar Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta yi tir da halin da bangaren lafiya na kasar ke ciki, kan yadda abubuwa ke kara tabarbar...
Rating :
5