Asusun bada agaji na kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ta ce ya kamata maza su ma su fara samin hutu akalla na makoni hudu tare da albashi a duk lokacin da matansu suka haihu domin dan da aka haifan ya samu kulan da ya kamata.
Wakilin asusun Unicef Mohammed Fall ya sanar da haka a taron wayar da kan mutane kan kula da yara kanana da aka yi a Abuja mai taken ‘‘Zubi mai amfani wajen kula da yaran Najeriya.”
Mohammed Fall ya ce watanni ukun da mata ke samu duk lokacin da suka haihu a Najeriya ba ya isa idan dai ana so yaro ya sami kulan da ya kamata.
Ya ce kamata ya yi iyaye su sami isasshiyar lokaci domin kula da yaron da suka haifa domin hakan zai taimaka wajen kuzarin da yaro ke bukata musamman idan sun fara makaranta.
Source: Premium Hausa
Title :
Afara Bawa Maza Hutun Wata Uku Da Albashi Idan Matansu Sun Dauki Ciki-Jami'in Unicef
Description : Asusun bada agaji na kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ta ce ya kamata maza su ma su fara samin hutu akalla na makoni hudu tare...
Rating :
5