An ware ranar Alhamis ta biyu a cikin watan Oktoban kowacce shekara a matsayin ranar gani ta duniya.
Rana ce da aka kebe musamman domin jawo hankalin al'ummar duniya kan makanta da cututtukan da su ka shafi rashin gani.
Hukumar lafiya ta duniya wato WHO, ita ta kebe wannan rana inda ita da wasu kungiyoyi masu zaman kansu ke gudanar da bikin zagayowar ranar ta hanyar wayar da kan mutane a kan illar makanta da kuma yadda za a kare kai daga kamuwa da lalurar makanta.
An kuma kebe wannan rana ne domin a nuna wa jama'a muhimmancin gani a rayuwar dan Adam.
Ana kuma amfani da wannan rana wajen taimakawa masu fama da lalurar makanta.
Wani bincike da aka gudanar ya gano cewar, ana samun raguwar kamuwa da cutar makanta a duniya ma baki daya.
Wani likita a Najeriya, Dr. Ibrahim Kana, ya shaida wa BBC abubuwa uku da ke janyo cutar makanta, inda ya ce akwai yanar ido da dundumi da kuma cutar da ke dashe ganin gari sosai wadda ke tilastawa mutum sanya tabarau.
Dr.Kana ya ce mutane za su iya kare kansu daga kamuwa da cutar makanta matukar sun kiyaye dokoki da kuma zuwa asibiti a kan lokaci domin a gwada su.
Najeriya na daga cikin kasashen da ke gudanar da bikin zagayowar wannan rana, inda ake bi lungu da sako na kasar ana wayar da kan mutane a kan muhimmancin zuwa asibiti domin gwajin idanu da zarar an ji ba daidai ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Adadin Makafi Na Raguwa A Duniya
Description : An ware ranar Alhamis ta biyu a cikin watan Oktoban kowacce shekara a matsayin ranar gani ta duniya. Rana ce da aka kebe musamman domin jaw...
Rating :
5