Shahararriyar ‘yar wasan fina-finan Hausa Fati SU ta ce akwai wasu abubuwa guda uku da ke burgeta a farfajiyar Kannywood da wasu guda uku da ke ci mata tuwo a kwarya yayin shirya fim.
Da take zantawa da PREMIUM TIMES HAUSA, Fati SU ta ce tana matukar jinjina wa jaruman kannywood da sauran yan uwanta da ke harkar fina-finai a farfajiyar.
Ta shaida mana wadansu ababe uku da ke matukar burgeta a farfajiyar.
1 – Taimaka wa juna. Idan Har kana wannan farfajiya na Kannywood zaka ga ana tattaimaka wa juna musamman idan kai sabon shiga ne. Ana amfana da haka mussamman daga wurin dadaddu a harkar.
2 – Rashin yi wa juna bakin ciki. Ko da yake kowa da yadda yake ganin abin, ni dai a nawa ganin sai dai a sami rashin jituwa amma son juna ya fi yawa a tsakanin mu. Rashin bakin ciki ga juna musamman idan baka dade ba da Fara harkar. Manyan za su yi ta taimaka maka kaima tauraron ka ya shana.
3 – Hadin Kai – Duk inda kaga dan wasa to zaka ga ana tafiya tare ne. Ko da akwai na ciki amma dai ana tare.
Uku dake ta da mini hankali
1 – Tilasta maka sai ka kware – Duk da abune mai kyau amma gaskiya wata rana sai kaji kaman ka sa Ihu idan Direkta ya matsa sai kayi yadda ya kamata.
2 – Idan an hada ka da jarumi ko Jaruma a wasa, musamman idan yana gaba da kai sai kaji kamar ba ka komai saboda kwarewarsu. Sai dai yana da amfani domin shima hakan gwaji ne.
3 – Idan wurin da za ayi fim din ba dadi sai kaga ka kosa a gama fim din kaje ka huta.
Source: Premium Hausa
Title :
Abubuwa Uku Dake Burgeni Da Wadda Ke Tadamin Hankali A KannyWood-Fati Su
Description : Shahararriyar ‘yar wasan fina-finan Hausa Fati SU ta ce akwai wasu abubuwa guda uku da ke burgeta a farfajiyar Kannywood da wasu guda uku da...
Rating :
5