Ana ganin tsakanin kashi daya zuwa uku na mutane ba su damu da jima'i ba, ma'ana ba sa jin sha'awa a tare da su.
Tun tsawon shekaru Stacey na damuwa game da yadda ba ta son kwanciya da kowa, har mijinta ma. Kamar yadda ta yi bayani a anan likitanta ne ya shaida mata hakan.
Tun tsawon lokaci, na yi tsammanin ko ba ni da lafiya, shi yasa ma ba na son yin jima'i da kowa.
Kawayena suna yawan magana game da irin samarin da suke so su yi jima'i da su, amma ni ba na ma tunanin wani da yake birgeni ko nake sha'awar jima'i da shi.
A lokacin da na kai shekara 20 ne na fara fahimtar hakan, amma ban taba yin magana da kowa a kan haka ba, saboda za su yi tsammanin ni farin shigar abin ce shi yasa ma kawai na yi shiru da bakina.
Na hadu da saurayina wanda kuma shi ne mijina yanzu a lokacin da nake shekara 19, amma a lokacin ban san mene ne rashin sha'awar jima'i ba, kawai na yi tsammanin don ba sa son abin a raina ba ne.
Ina tunanin cewa, "Ina matukar son wanann mutumin, kuma idan ya ce yana sona zan amince da shi dari bisa dari, saboda ina so na zauna da shi har karshen rayuwata, amma kuma me yasa ba na son kwanciya da shi? Abin da mamaki".
Sai dai na mijina ya fahimce ni sosai ta yadda bai taba takura min sai ya kwanta da ni ba, ya ce zai hakura har sai lokacin da ni da kaina na bukata.
Kuma bai taba gajiya da halayyata ba.
Amma fa dabi'un al'ada na nuna cewa babban abu a zaman aure shi ne saduwa da kuma haihuwa. Don haka na kan damu cewa yanzu haka mutane suna tsammanin ina auratayya da mijina ina har ma zan haihu.
Sai kawai na fara munanan mafarkai cewa mijina zai guje ni wata rana ya samu wacce ke kama da ni amma wacce za ta ba shi hakkinsa na aure, har sai da ta kai ta kawo abin na daga min hankali.
Kawai sai na sawa raina cewa dole na magance wannan matsalar.
A lokacin na kai shekara 27 ko 28.
Babban kuskuren da na yi shi ne yin bincike a yanar gizo don gano dalilan da za su iya jawo min rashin son jima'i. Wannan kuskure ne babba.
Ana iya samun kananan matsaloli kamar rashin daidatuwar kwayoyin halitta, amma wanda ya daga min hankali shi ne kansar kwakwalwa ma na iya jawowa.
Kawai sai na firgita, na fara cewa: "Shi kenen kansar kwakwalwa ce za ta kashe ni."
Sai na tafi wajen likita na ce, "Abu ne mai tsanani? Zan iya mutuwa?"
Sai ta ce, "Kwantar da hankalinki, ba komai ba ne rashin sha'awa ne kawai."
Sai na ce, "Me hakan ke nufi?"
Sai ta nuna min bayanin hakan a intanet - sai na ji na samu nutsuwa.
Ban taba sanin akwai matsalar rashin son jima'i ba.
Sai na yi wa mijina bayani kan hakan na kuma ce masa.
Ya fahimce ni ya kuma sake ba ni goyon baya.
Shekarata 60 kuma ban taba haduwa da wani mutum da ba ya son jima'i ba, ban taba sanin akwai wannan matsalar ba," in ji wata Lucy.
A lokacin da na fara gano cewa ni ba na son jima'i, na yi koakrin gayawa wasu mutane kadan, wasu sun sake mun yi maganar sosai kuma na kadu da abubuwan da na ji, akwai lokacin da wasu 'yan makarantarmu suka shirya mana fitar dare don mu je mu gwangwaje da 'yan mata don sun ga ban taba neman wata mace ba, ba su san cewa matsala ce ke hana ni ba." In ji Scott
Rashin son jima'i wani ciwo ne kuma akwai mutane da dama da suke fama da haka, da zarar sun samu dangantaka da wani, za su ji sun samu nutsuwa idan suka yi jima'i da su. Amma ni kuma, duk lokacin da muka samu alaka da wani, sai na dinga ji a jikina kar na yi, "wata zuciyar na ce min kar ki yi haka."
Kamar wasan yara, mutanen da nake tattaunawa da su ko da yaushe suna ce min,"Ikon Allah, to ta yaya za ki samu 'ya'ya kenan?
Kwarai kuwa, a kwai hanyoyi da yawa da zan iya samun 'ya'ya idan ina bukatarsu,
Shekara uku zuwa hudu da suka shude ne kawai na fahimci wani abu game da rashin son jima'i. Ina son . Kuma shi ne abin da ya taimakamin na fahimci yadda dabi'ata take da kuma yadda zuciyata take aiki.
Abin dariya, kafin na gano yanayina na rashin son jima'i mijna yana kirana da State Ace.
Source: BBC Hausa