Wani kwararren likitan kashi da kwakwalwa Biodun Ogungbo ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta horar da masu gyaran kashi na gargajiyya saboda kawar da masalolin da mutane kan yi fama da su bayan an gyar musu karaya ko targade.
Biodun ya fadi haka ne ranar Laraba da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai inda ya kara da cewa sau da yawa bayan masu gyaran kashin gargajiyya sun gama aikin su akan sami matsaloli da dama kaman rashin sa’an daidaita kashin yadda ya kamata, rashin motsawan jini yadda jijiyoyin jikin mutum za su yi aiki yadda ya kamata, samun raunin da ake kira da ‘Tetanus’ da sauransu.
Ya ce hakan na faruwa ne saboda rashin sanin hanyoyin da ya kamata abi wajen gyara kashi ba tare da an sami matsala ba.
Biodun Ogungbo yace horar da masu gyaran kashi na gargajiyya akan yadda ya kamata a gyara kashin zai taimaka wajen ceto rayukan mutane da dama musamman mazauna karkara. Saboda haka ya ce za su taimaka wa mutane samun kulan da ya kamata idan sun karye ta hanyar rage kashi 5.7 bisa 100 na farashin kudin gyaran kashi.
Source: Premium Hausa
Title :
A Guji Masu Daurin Gargajiya
Description : Wani kwararren likitan kashi da kwakwalwa Biodun Ogungbo ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta horar da masu gyaran kashi na gargajiyya sabo...
Rating :
5