Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta bayyana cewa nan da kwanaki 10 za a kammala kwaso Alhazan Najeriya
kakaf.
Zuwa yanzu dai an dawo da Alhazai 42,126 a cikin sawu 100 na jiragen da suka yi aikin kwaso Alhazan. Haka wani jami’in hukumar ya bayyana.
Shugaban Hukumar, Abdullahi Mohammed, ya bayyana cewa yana godiya ga Allah domin yanzu wasu matsaloli da Najeriya ta rika fuskanta a shekarun baya, a yanzu duk sun zama tarihi.
Wasu daga cikin matsalolin kamar yadda Mohammed ya bayyana, sun hada da Bacewar Alhazai, hatsaniya a filin jirgi a Jidda, turereniyar hawa motoci, rashin abinci mai inganci ga Alhazai, rashin wurin kwana mai tsafta duk sun zama tarihi.
Ya kuma yi gargadi ga jami’an hukumar sa cewa su rika hakuri da fushin da wasu Alhazai ke nunawa ko hucewa kan su.
“Wasu sun dade rabon su da gida, sun matsu su koma, wasu kuma dan guzirin na su ne ya kare.”
Source: Premium Hausa
Title :
Zamu Kammala Kwaso Alhazai Nan Da Kwana Goma-Hukumar Alhazai
Description : Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta bayyana cewa nan da kwanaki 10 za a kammala kwaso Alhazan Najeriya kakaf. Zuwa yanzu dai an dawo da Al...
Rating :
5