A ranar Talatar nan ne za a rantsar da sabon shugaban kasa a Angola, Joao Lourenco, wanda zai maye gurbin Jose Eduardo Dos Santos, wanda ya shafe kusan shekara 40 a kan mulki.
Ta wani fannin za a iya cewa wannan wani tarihi ne na sauyin mulki a kasar, inda shugaba daya tilo da miliyoyin 'yan Angola suka sani a kan mulki, zai yi bankwana da kujerar mulki.
To amma fa, kila hakan da wuya ya kawo wani gagarumin sauyi a kan alkiblar tafiyar da horkokin mulkin kasar ta Angola.
Sabon jagora, Joao Lourenco, ya kasance a gaba-gaba a zuciyar jam'iyya mai mulki ta MPLA tsawon shekara da shekaru.
Mutumin da zai gada a mulkin, Jose Eduardo Dos Santos, zai ci gaba da rike iko da jam'iyyar, bayan ikon nada shugaban 'yan sanda da na soji da zai ci gaba da rikewa, sannan kuma masu suka na cewa 'ya'yansa, kamar matar da ta fi arziki a Afirka Isabel Dos Santos, an tsara yadda za ta rike ragamar tafiyar da tattalin arzikin kasain mai na Angola akwai gagarumin bambanci tsakanin jama'ar kasar, talakawa da masu hali.
Sabon shugaban kasar da tsohon tsarin gwamnatin za su fuskanci bukata ko kalubale na canji na ainahi.
Jam'iyyar MPLA ita ce ke mulkin Angola tun da ta samu 'yanci daga Portugal a 1975.
Kasar ta yi fama da yakin basasa na tsawon shekaru da 'yan tawayen tsohuwar kungiyar UNITA (National Union for the Total Independence of Angola ), ta marigayi Dakta Jonas Savimbi.
Yakin da ya zo karshe bayan halaka madugun 'yan tawayen, a wani kwanton-bauna a ranar 22 ga watan Fabrairun 2002.
Bayan kisan shugaban 'yan tawayen ne kungiyar ta rikide ta zama jam'iyyar siyasa, inda yanzu ta zama ta biyu a kasar ta Angola.
Source: BBC Hausa
Title :
Zaa Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Angola
Description : A ranar Talatar nan ne za a rantsar da sabon shugaban kasa a Angola, Joao Lourenco, wanda zai maye gurbin Jose Eduardo Dos Santos, wanda ya ...
Rating :
5