Gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya don gurfanar da mutanen da ake tuhuma da zama mayakan kungiyar Boko Haram sama da 1,600 a gaban kotu.
Ministan Shari'a na kasar Barista Abubakar Malami ya shaida wa BBC cewa za a fara yi wa mutanen shari'a ne a cibiyoyi daban-daban da ake tsare da su daga watan gobe.
Ma'aikatar shair'ar ta kara da cewa an bayar da shawarar sakin mutane 220 da ake zargi da zama 'yan Boko Haram saboda babu wata cikakkciyar shaida da ke nuna hakan.
A cewar ministan, an samu alkalai na musamman guda hudu wadanda za su yi shari'ar.
Ya kara da cewa kawo yanzu an kammala shari'ar 'yan Boko Haram 13, an samu tara da laifi, sannan kuma wasu manyan kotunan tarayya na ci gaba da shari'ar mutum 33.
Rundunar sojin kasar dai ta ce ta kusa murkushe 'yan kungiyar ta Boko Haram bayan da ta kwace yankunan da a baya suka mamaye.
Sai dai har yanzu 'yan kungiyar na kai hare-aren kunar-bakin-wake a wasu yankuna na jihar Borno lamarin da kan haddasa asarar rayuwa.
Source: BBC Hausa
Title :
Za'a Fara Shari'ar 'Yan Boko Haram 1,600
Description : Gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya don gurfanar da mutanen da ake tuhuma da zama mayakan kungiyar Boko Haram sama da 1,600 a gaban kotu. Mi...
Rating :
5