Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris, ya ba da umarnin a cire shingayen binciken ababen hawa a duk fadin kasar.
Ya ba da umarnin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa CSP Jimoh O. Moshood ya aikewa manema labarai.
Sanarwar ta ce, an umarci a cire shingayen ne musamman na hanyar birnin Legas zuwa Ibadan, da Shagamu zuwa Benin, da Benin zuwa Onitsha, da Okene zuwa Abuja.
Sai kuma Kaduna zuwa Kano, da Katsina zuwa Kano, da Otukpo zuwa Enugu, da Enugu zuwa babban hanyar Fatakwal.
Sanarwar ta ce Sufeton ya bukaci a cire shingayen nan take ba tare da bata lokaci ba, haka kuma an bukaci ayi hakan ne dan saukakawa 'yan kasuwa da jama'a zirga-zirga daga arewaci zuwa kudancin kasar.
A karshe sanarwar ta bukaci gwamnatocin jihohi, da kananan hukumomi, hukumar karbar haraji ta jihohi da kungiyar direbobi, da kungiyar 'yan kasuwa da su bai wa jami'an tsaron hadin kai don tabbatar da sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Sanarwar ta ce Sufeton 'yan sandan Najeriyar ya dauki wannan mataki ne don tabbatar da tsaron 'yan Najeriya da kuma tabbatar da doka da oda.
Source:BBC Hausa
Title :
Za'a Cire Shingayen Binciken 'Yan Sanda
Description : Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris, ya ba da umarnin a cire shingayen binciken ababen hawa a duk fadin kasar. Ya ba da u...
Rating :
5