Yanzu mun fara warware cukurkudaddun al'amuran kwakwalwa, wadanda ke ba mu damar amsa rikirkitattun tambayoyi, kamar "mene ne nisan tunani?
Lokacin da aka bijiro masa da tambayar barkwanci, don ya bayyana yadda kwakwalwa ke aiki cikin kalmomi biyar, masanin kimiyyar aikin kwakwalwa Steven Pinker bai yi nawa ba.
"Kwayoyin halittar kwakwalwa na bijiro da tsarin ayyuka," a amsarsa. Kokari ne mai kyau, amma hakikanin abin da take yi, shi ne maye gurbin cukurkudadden al'amari da wani rudanin.
An dade da sanin cewa kwayoyin halittar kwakwalwa kan aike da sakonni ga juna ta hanyar tartsatsin ankararwar lantarki, kuma a yanzu muna da dimbin fasahar kere-keren tattara bayanai kan ayyukan tsare-tsare tun daga sandunan tartsatsin lantarkin kwakwalwa da ke kan rufin kokon kai har zuwa maganadisun zuko bayanai da ke gano sauye-sauyen iskar oxygen da ke cikin jini.
Sai dai ko da an tattara wadannan bayanai, ma'anar wadannan tsare-tsare har yanzu a cukurkude take. Alamu sun nuna suna juyin takun kidan da ba ma iya ji, karkashin ka'idojin da ba mu sani ba.
Masana kimiyyar tantance tasirin kwakwalwa kan dabi'u sun yi bayanin tsare-tsaren sakon jijiya, inda suka samu nasarar warware sarkakiyar.
Suna ta kokarin fitar da wasu dokoki, wadanda suka hada da idan kwayoyin halitta na barin kwakwalwa za su bijiro da farin ciki ya dogara ne kan abin da ke wakana a lokacin.
"An dan samu tsaiko, amma a shekara 10 da suka gabata gungun masu bincike daban-daban a fadin duniya na kara kokarin kan wannan lamari''.
Ta yiwu ba za mu samu damar kai wa ka ga cikakkiyar sarkakiyar ba, kamar yadda suka fahimta, amma ta hanyar kokarin shigar da bayananmu, za mu fara gano daidaikun hanyoyin da mabambanta tsare-tsare suka yi daidai da mabambanta ayyuka.
Albert Lee da Matthew Wilson, na Cibiyar Fasahar kere-kere ta Massachusetts (MIT) su suka fara taimakawa wajen fitar da ka'idoji cikin shekarar 2002.
Haka aka yi ta ci gaba. Da farko mun tattara bayanan kwakwalwar bera, tunda tana daya daga cikin dabbobiun da ke kusantarmu a matakin rayuwa na jerin halittun da ke karakaina cikin rudani.
Nazarin daukacin kwakwalwa na da wuya, don haka sai mu mayar da hankali kan muhimmin bangaren da ke kai-kawo a tunani da adana sakonni.
Idan ka taba jin labarin wannan sashe tuni ta yiwu a ce mashahurin sakamako ya yi nuni da cewa direbobin tasin Landan suna da babbar matattarar tuntuni bisa la'akari da tsawon lokacin da suka shafe suna kai-kawo a titunan katafaren birnin London.
Tsawon lokacin da direbobin tasi ke dauka wajen kai-kawo a titunan birni, shi zai fadada ayyukan kwakwalwarsu da karin kara-kaina a tunani
Duk da cewa bera na tattare da cukurkudaddun al'amura da aka tattara bayanai kansu, kuma a lokaci guda kwayoyin halittar zirin sarrafa bayanai da tunani ke harbawa.
Kwayoyin halittar na harba bisa tartibin tsarin lissafi, wanda ya daidaita da kowane silin cukurkude-cukurkuden.
Bayan kwayoyin halittar na da saukin fahimta, amma yanzu muna da bayanai biyu da ke warware kulle-kullen.
Gwajin tartibin lissafi ta hanyar cusa masa bayanan da aka tattara sababbi, don gano inda bera yake a lokacin da aka tattara bayanan sarrafa zirin sarrafa bayanai da tunani.
Ba za mu samu damar warware cukurkudaddun al'amuran gaba daya ba, saboda har yanzu ba mu fahimci ka'idojin ba, sannan ba za ta iya taimaka mana wajen fahimtar tsare-tsaren da ba da daga wannan bangaren kwakwalwar suke kara-kaina ba, sai dai har yanzu dai ita makama mai karfi.
Misali ta hanyar amfani da dabarar gungun masu binciken zai iya nuni da cewa jerin kwayoyin halittar da ke harbawa a kwakwalwar bera lokacin barci bayan kara-kainar zirin sarrafa bayanai (kuma muhimmiyar kwatanceceniya, wadda ba ta barci ba a yanayin annashuwa kafin harbawar zirin sarrafa bayanai).
Abin sha'awar shi ne, shi ne tartibin ayyuka na maimaituwa cikin sauri lokacin barci da kimanin juyi 20 da sauri-sauri. Wannan na nufin bera ya fi shiga rudunanin kwakwalwa lokacin barci cikin kankanen lokaci in an kwatanta da rayuwar farke.
Za a iya danganta lamarin da halarto da al'amura lokacin barci ta hanyar sarrafa tunani, wanda ka iya taimaka wa bera ya tattara natsuwa wajen koyon dabara.
Kuma a gaskiya kai-kawon tunani na kara sauri ne ta yadda zai ba mu haske kan boyayyun al'amura ko al'amuran da suka shafi rayuwarmu "su bayyana a idanunmu''.
Idan ba a yi musu shamaki ba, sai tunaninmu ya bibiya hanyoyin da aka saba da su tare da "hanzarin gabatowa."
Ayyukan da suka gabata sun yi nuni da cewa cukurkudaddun al'amura kan iya juyawa baya, kamar yadda za su zabura zuwa gaba, al'amarin da ke nuni da cewa beraye na tunanin mafita, kalmar a ce yadda za su kai ga karshe cukurkudaddiyar hanya.
Bera na da basirar gane cukurkudaddiyar hanya sau 20 da sauri lokacin da yake barci fiye da farkwarsa
Dabbaka dabaru irin wadannan, wadanda suka yi daidai da muhimmin tsarin musamman na tartibin alkaluman lissafin algorithms, da ke da manufar warware matsalar kwakwalwar mara lafiya da ke tsare ko halin rai kwakwai, mutu kwakwai.
Irin wadannan marasa lafiya ba za su iya motsa jkikinsu ba, duk da haka ta yiwu kwakwalwarsu na aiki suna sane da halin da suke ciki, kuma suna jin mutane na magana a daki guda. Na farko, likitoci kan tambayi marasa lafiya su yi hasashen yanayin aikin wani bangare na kwakwalwa kamar rumbun sarrafa sakonni.
Bayanan da aka tattara sai aka yi fiolla filla da su don fahimtar aikin kwakwalwa, wanda ke wanzuwa a bangaren kwakwalwar na musamman klamar rumbun sarrafa sakonni. Bayan da aka tattara aka yi nazarinsu don gano yadda aikin kwakwalwa ya yi daidai da wasu dabaru.
Lokacin bibiyar hotunan kwakwalwa nan gaba, marasa lafiya za su iya sake hasashen irin wadanan al'amuran don amsa muhimman tambayoyi.
Misali za sa su kudura cewa suna wasan kwallon tennis sai su ce eh, kuma suna kewaye gidansu sai su ce a'a itga sadarwar sakonnin farko tun bayan jin rauninsu.
Akwai sauran dabaru, wadanda daukacinsu na kimiyya ne da ake amfani da su wajen tantance aikin cikin kwakwalenmu, kuma gwajin aikace tamkar kulla dangantakar kwakwalwa da kwamfuta.
Idan nan gaba mai shanyayyen jiki na son juya akalar mutumin robot ko ma na wani mutumin, ta hanyar alakar kwakwalwa, to ya dogara ne kacokam kan dabaru iri guda na sarrafa bayanai da tabbatar da ma'anarsu a aikace. Yanzu dabarun an tabbatar za a iya aiki da su, yiwuwar za ta bayar da mamaki.
Source: BBC Hausa