Akalla Musulmai 'yan kabilar Rohingya 290,000 daga jihar Rakhine a kasar Myanmar suka ketara zuwa kasar Bangladesh mai makwabta cikin makonni biyu da suka wuce.
Musulmin 'yan gudun hirar na cewa sojojin Myanmar su na kona kauyukansu- zargin da sojojin ke musantawa.
Tashin hankalin ya fara ne a ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata lokacin da wata kungiyar gwagwarmayar 'yan Rohingya ta kai wa wani ofishin 'yan sanda hari a arewacin jihar Rakhine.
Daga nan ne sai sojojin Myanmar suka fara murkushe su, kamar yadda 'yan kabilar Rohingya suka bayyana.
Sai dai gwamnatin kasar ta musanta hakan, inda ta ce ta na yakar "'yan ta'addan" Rohingya ne kawai.
An kama 'babban kwamandan IS' a KanoYadda ake cinikin 'yan aiki a intanet
'Yan Rohingya wadanda galibinsu Musulmi ne da ba su da kasa, na rayuwa ne a kasar Myanmar wacce mabiya addinin Buddha ke da rinjaye.
Kungiyoyin ba da agaji a Bangladesh sun ce adadin 'yan gudun hijirar Rohingya da ke shiga kasar ya wuce wanda za su iya dauka, yayin da ake cewa akwai dubban 'yan Rohingya da ke tsaye a gefen hanya, suna rokon abinci.
Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AP ya ce, ya hangi wani mutum da ya yanke jiki ya fadi yayin da yake bin layin abinci.
Har ila yau, wani wakilin BBC ya ce a kan idonsa aka cinnawa wani kauyen Musulmin Rohingya wuta a jihar Rakhine da ke Myanmar.
Ana ci gaba da yin kalaman Allah-wadai game da yadda gwamnatin Myanmar ta ke musgunawa Musulmi tsiraru 'yan kabilar Rohingya.
Har yanzu babu adadin yawan Musulmi 'yan Rohingya da suka rasa rayukansu sanadiyyar rikicin
Shugabannin kasashen duniya sun bukaci Misis Suu Kyi, wadda ta taba lashe kyautar Nobel ta Zaman Lafiya da ta fito ta yi magana a madadin 'yan Rohingyan.
Koda yake ta amsa kiran daga bisani, inda ta ce "kafofin yada labarai na kara gishiri game da abin da yake faruwa a jihar Rakhine."
Daga nan ta ce "ana kula da duk wani mutum da yake zaune a Myanmar dan kasa da kuma bako, muna iya kokarinmu duk da cewa ba mu da wadata sosai."
Source: BBC Hausa
Title :
Yadda Ake Musguna Wa Musulmi A Myanmar
Description : Akalla Musulmai 'yan kabilar Rohingya 290,000 daga jihar Rakhine a kasar Myanmar suka ketara zuwa kasar Bangladesh mai makwabta cikin ma...
Rating :
5