An gano wata halittar ruwa mai dogayen hakora wadda ba a taba gani ba bayan guguwar Harvey a Amurka.
Wata mata mai suna Preeti Desai ta ga wannan halittar a gabar tekun Texas kuma ta sa hoton a shafin Twitter, tana neman agajin tambayoyi.
Matar ta tura hotuna da yawa sai ta rubuta, ''To masan ilimin halittu na Twitter, mene ne wannan?''
Wannan na daya daga cikin halittu tara na kasar Indiya wadanda ba a taba ganin irin su ba.
An gano sababbin nau'in halittu guda 5000.
An tura tambaya ga masanin illimin halittu da kiwon kifi Dokta Kennith Tighhe, wanda yake tunanin maciji ne mai hakora masu kaifi.
Ya kuma ce halittar za ta iya zama nau'in kifi mai kama da maciji.
Sai dai ya ce irin wannan halittun guda uku ne da ake samu a Texas, wadanda suke da manyan hakora masu tsini.
Ana kyautata zaton cewa guguwar Harvey da iska mai karfi ne sanadiyyar kawo wannan halittar gabar teku.
Halittar da a ke kira Tusky Eli ana samunta ne a cikin Tekun Atlantika.
Desai wadda ta je gabar tekun don nazarin girman barnar da guguwar ta jawo, ta shaida wa BBC cewa: ''Ba a taba zaton samun wannan halittar ba, ba abin da aka saba gani ba ne a bakin teku.
"Ina tsammanin halittar ta fito bakin tekun ne daga tsakiyar tekun."
Ta ce, ''Abin da ya fara zuwa raina shi ne zakuwar sanin mene ne abin.''
Desai ta kara cewa, "Na dauki hoton ne na tura a shafin Twitter saboda na san masana kimiyya da dama suna amfani da shi, daga nan ne wata kawata ba tare da bata lokaci ba ta kira Dokta Tighe.''
Ta ce ''Ina bibiyar masana kimiyya da dama, akwai al'umma mai kyau da yawa, wadanda suke taimakawa sosai, tun ba a kan tambayoyi da suke da alaka da son fahimtar rayuwar halittu ko tsirrai ba."
A karshe ta ce ta bar wannan halitta a wurin da ta tsince ta wato bakin tekun, a tunanin cewa za ta koma inda ta fito.
Source: BBC Hausa
Title :
Wata Halittan Da Ba'a Taba Ganiba Ta Bullo A Amurka
Description : An gano wata halittar ruwa mai dogayen hakora wadda ba a taba gani ba bayan guguwar Harvey a Amurka. Wata mata mai suna Preeti Desai ta ga ...
Rating :
5