An daure wani tsohon shugaban kamfanin hada magunguna a Amurka, Martin Shkreli bayan kotu ta same shi da laifin kasancewa barazana ga rayuwar jama'a.
Mista Shkreli ya yi tayin ba da ladan dala dubu biyar ga duk mutumin da ya samo masa silin gashin Hillary Clinton.
A cikin makon jiya ne, jim kadan kafin Mrs. Hillary Clinton ta fara wani rangadi kan wani littafi, Shkreli ya buga a shafinsa na Facebook cewa zai biya ladan dala dubu biyar ga duk mutumin da ya tsigo masa silin gashin kanta.
Lauyansa ya fada wa kotu ce ai bayanin da ya wallafa na samun kariya daga 'yancin fadar albarkacin baki, sai dai alkalin kotu ta ce a'a.
Kafofin yada labarai a kasar na yi masa lakabi da "mutumin da aka fi tsana a Amurka" bayan kamfaninsa mai suna Turin ya tsawwala farashin wani maganin ceton rai.
An ba da belin Shkreli, ina a yanzu yake jiran hukuncin kara biyu kan almudahana wadanda kuma ba su danganci abin kunyar tsuga farashin magani ba.
Da take bayyana shawarar sauke belin Shkreli, mai shari'ar ta ce tayin biyan lada kan gashin Hillary Clinton neman tijara ce, kawai don biyan kudi, kuma hakan ya nuna Mista Shkreli a matsayin wani hatsari ga jama'a.
Source: BBC Hausa
Title :
Wani Mai Magani Yace A Tsigo Masa Gashin Clinton
Description : An daure wani tsohon shugaban kamfanin hada magunguna a Amurka, Martin Shkreli bayan kotu ta same shi da laifin kasancewa barazana ga rayuwa...
Rating :
5