Koriya Ta Arewa na ci gaba da musayar zafafan kalamai da Amurka, inda shugaba Kim Jong-un ya bayyana Donald Trump a matsayin mai tabin hankali.
Kamfanin dillancin labaran Koriya Ta Arewa da ke birnin Pyongyang ya ambato Kim Jong-un na cewa shugaban Amurka zai yaba wa aya zaki saboda jawabin da ya yi tun farkon wannan mako a Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Donald Trump ya fada wa taron cewa idan tura ta kai Amurka bango, to za ta kare kanta, kuma sai ta yi raga-raga da Koriya Ta Arewa.
Ya yi wa Kim Jong-un shakiyanci ta hanyar kiransa da 'Mai Roket".
A ranar Alhamis ma, Donald Trump ya sanar da kakaba karin takunkumai a kan Koriya Ta Arewa, har ma ya yaba wa mahukuntan China.
"Ina mai matukar alfaharin fada muku, kamar yadda mai yiwuwa kuka ji dazun nan cewa babban bankin China ya sanar da sauran bankunan kasar cewa su daina hulda da Koriya Ta Arewa," in ji shi.
Donald Trump ya ce bankunan kasashen waje za su fuskanci zabi karara cewa ko dai su yi hulda da Amurka ko kuma su yi kasuwanci da gwamnati maras bin doka a Koriya Ta Arewa.
Ya bayyana dokar shugaban kasa da ya sanya wa hannu a matsayin wani sabon abu mai karfi da ya ce za ta yi magani wata kasa guda, kuma ita ce Koriya Ta Arewa
Source: BBC Hausa
Title :
Trump Nada Tabin Hankali-Kim Jong Un
Description : Koriya Ta Arewa na ci gaba da musayar zafafan kalamai da Amurka, inda shugaba Kim Jong-un ya bayyana Donald Trump a matsayin mai tabin hanka...
Rating :
5