Rundunar sojin Najeriya ta musanta wasu rahotanni da ke cewa dakarunta sun kai hari tare da kashe mutane a garin Afaraukwu na madugun kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu.
A sanarwar da rundunar ta fitar ta karyata labarin da kungiyar ta IPOB take yadawa da ma wasu hotuna na mutane da ake cewa sojojin sun harba wadanda ake yadawa a intanet,a lokacin da sojojin suka yi wa kauyen Nnamdi Kanun dirar mikiya.
A martanin da sojojin suka yi sun ce babu wani abu makamancin haka da ya faru, illa dai wasu tsegarun kungiyar ta fafutukar kafa kasar Biafran ne suka datse hanya ga kwambar sojojin da ke kewaya birnin Umuahia na jihar Abia a jiya Lahadi da yamma, har ta kai da suna jifan sojojin da duwatsu da fasassun kwalabe, lamarin da ya yi sanadiyyar raunata wata mata da ke wucewa da kuma wani kofur na sojin.
Source: BBC Hausa
Title :
Sojojin Nigeria Sun Karyata Farmaki Kan 'Yan Biafara
Description : Rundunar sojin Najeriya ta musanta wasu rahotanni da ke cewa dakarunta sun kai hari tare da kashe mutane a garin Afaraukwu na madugun kungiy...
Rating :
5