A kalla mutum 22 ne suka rasa rayukansu lokacin da rudunar Sojin Najeriya ta kai samame gidan madugun kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu a jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya, kamar yadda dan uwansa ya shaida wa BBC.
"Sojoji sun isa gidanmu dauke da makamai da ayarin motoci kirar Hilux kimanin guda 20. Sun bude wa jama'a wuta a gidan wanda hakan ya sa kimanin mutum 22 sun rasa rayukansu," in ji Prince Emmanuel Kanu.
Har ila yau, ya yi zargin cewa sojojin sun lalata fadar mahaifinsu wanda basaraken gargajiya ne a yankin.
Hakazalika ya ce sojojin sun tafi da wadansu muhimman takardu na dan uwansa da kuma wadansu kayayyaki na gidan.
BBC ta tuntubi mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya ta 82, Kanar Sagir Musa, wanda ya ce ba shi da bayanin abin da ya faru, kuma ya bukaci mu ba shi lokaci ya yi bincike game da batun.
Sai dai ya ce batun jita-jitar za a janye sojoji a yankin ba gaskiya ba ne, kuma a ranar Juma'a ne sojojin za su fara atisaye na musamman a yankin, kamar yadda ya ce.
Ana ci gaba da zaman zullumi a yankin Kudu maso gabashiin Najeriya, inda aka samu wata hatsaniya tsakanin yan kungiyar neman kafa kasar Biafra ta IPOB da kuma sojin Najeriya da ke gudanar da wani atisaye a yankin. Abin da ya haddasa asarar rayuka da dukiya.
Source: BBC Hausa
Title :
Sojoji Sunkai Sumame Gidan Nnamdi Kanu
Description : A kalla mutum 22 ne suka rasa rayukansu lokacin da rudunar Sojin Najeriya ta kai samame gidan madugun kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra, ...
Rating :
5