Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce jiragenta sun kai hari kan maboyar mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
A wata sanarwa da daraktan watsa labaran rundunar Olatokunbo Adesanya ya aikewa manema labarai, ya ce a kwana na hudu da dakarunta suka kwashe suna kai hari da bama-bamai a maboyar 'yan kungiyar da ke dajin Sambisa, sun lalata kayayyakin 'yan kungiyar.
Ya kara da cewa jiragensu, samfurin Alpha Jet da F-7Ni, sun gano maboyar ta 'yan Boko Haram gabanin kai musu hari.
"An kai hare-haren ne domin ci gaba da karya lagon mayakan kungiyar ta yadda ba za su iya sake haduwa waje guda domi kai wa dakarunmu na kasa hari ba", in ji sanarwar.
Rundunar sojin Najeriya dai ta sha yin ikirarin cin galaba kan mayakan kungiyar ta Boko Haram, tana mai cewa ba su da katabus din kai manyan hare-hare.
Sai dai 'yan kungiyar na ci gaba da kai hare-hare na kunar bakin wake a arewa maso gabashin kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Sojin Nigeriya Sunyi Wa Boko Haram Ruwan Wuta
Description : Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce jiragenta sun kai hari kan maboyar mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno da ke arewa maso gabashin...
Rating :
5