Kakakin rundunar sojin Najeriya Janar Sani Usman ya ce ‘Yan Siyasar yankin Kudu Maso Gabas ne ke tunzura mutane yin sa-in-sa da sojoji.
” Abin takaici ne yadda wasu yan siyasa ke yin amfani da abubuwan da ke faru domin tunzura mutanen gari da Sojojin Najeriya a kasar nan.
Ya ce atisayin da sojoji ke yi a garin Aba ya kama ne amma ba wai don su takura wa jama’a ba. Sannan zasu gudanar da irin wannan atisayi a yanki Kudu maso Yamma.
Yayi kira ga jama’a da su ba sojojin hadin kai sannan su tabbata sun bi doka.
Source: Premium Hausa
Title :
'Yan Siyasan Kudu Maso Gabas Neke Tunzura Mutane
Description : Kakakin rundunar sojin Najeriya Janar Sani Usman ya ce ‘Yan Siyasar yankin Kudu Maso Gabas ne ke tunzura mutane yin sa-in-sa da sojoji. ” A...
Rating :
5