Mata sun fi yiwuwar rashin son jima'i ninki biyu idan aka kwatanta su da abokan zamansu maza, in ji wani rahoto kan yadda ake jima'i a Birtaniya.
Rahoton ya gano cewa a yayin da mata da miji ke nuna rashin sha'awar yin jima'i a lokacin da suke kara manyanta, ita macen takan ji ba ta sha'awar yin jima'in saboda dadewar da aka yi tare.
A takaice, rashin isasshiyar lafiya da shauki tsakanin mata da miji yana yin tasiri wurin sha'awarsu ta yin jima'i.
Binciken ya yi nazari ne kan maza 5,000 da mata 6,700 inda aka wallafa shi a BMJ Open.
Manazartan na Burtaniya sun ce ya kamata a yi bincike a kan mutumin da ke fama da rashin sha'awar jima'i, maimakon bai wa mutum magani.
'Radadi da kuncin rayuwa'
Wata masaniyar ilimin jima'i Ammanda Major ta ce rashin sha'awar yin jima'i ba wata cuta ba ce, kuma akwai hanyoyi da dama da suka kamata mata da mazaje ke bukatar sauyi.
"Rashin sha'awar jima'i ba wani abin damuwa ba ne ga wasu, amma ga wasu hakan kan sanya su fuskantar radadi da kuncin rayuwa," in ji ta.
Jumilla, kashi 15 na maza da kashi 34 na matan da aka yi bincike a kansu sun ce sun daina sha'awar yin jima'i tsawon wata uku ko sama da haka a shekara daya.
Mazana daina sha'awar jima'i ne tsakanin shekara 35-44 yayin da daina sha'awar jima'in mata ke kai wa kololuwa tsakanin shekara 55 zuwa 64.
Source: BBC Hausa
Title :
Sha'awar Jima'in Mata Na Raguwa In Aka Kwatanta Dana Maza
Description : Mata sun fi yiwuwar rashin son jima'i ninki biyu idan aka kwatanta su da abokan zamansu maza, in ji wani rahoto kan yadda ake jima'i...
Rating :
5