Real Madrid za ta fara wasan farko a cikin rukuni a gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana a ranar Laraba a kokarin kare kambunta.
Madrid wadda ke da kofin guda 12 a tarihi, za ta karbi bakuncin APOEL Nicosia a Santiago Bernabeu, kuma wata kila Cristiano Ronaldo ya buga karawar.
Ronaldo bai buga wa Madrid wasa hudu ba, sakamakon dakatar da shi da aka yi, bayan da ya ture alkalin wasa a karawa da Barcelona a gasar Spanish Super Cup.
Sai dai hukuncin hana shi buga wa Madrid wasa biyar bai shafi na gasar Zakarun Turai ba, kuma saura wasa daya ya kammala hukuncin da hukumar kwallon Spaniya ta yanke masa.
Madrid ta buga wasa 14 a jere a gida ba a doke ta ba a gasar ta Zakarun Turai, tun bayan rashin nasara da ta yi a hannun Schalke a 2015.
Source: BBC Hausa
Title :
Ronaldo Zaiyi Wasa Wa Madrid Ranan Laraba
Description : Real Madrid za ta fara wasan farko a cikin rukuni a gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana a ranar Laraba a kokarin kare kambunta. Madrid wa...
Rating :
5