Cristiano Ronaldo bai fara wasannin cin kofin Spaniyar La Liga da kafar dama ba, yayin da har yanzu bai ci kwallo ba a gasar.
Ronaldo bai buga wasa hudu da aka fara kakar bana ba, sakamakon dakatar da shi wasa biyar da aka yi kan jan katin da aka yi masa a karawa da Barcelona a Spanish Super Cup.
Dan kwallon ya fara buga wa Madrid La Liga a karawar da Real Betis ta yi nasara da ci daya mai ban haushi a ranar Laraba, inda ya kai hari sau 20, amma bai ci kwallo ba.
A wasan mako na shida a gasar ta La Liga Ronaldo ya buga wa Madrid wasa na biyu, inda ta yi nasarar doke Deportivo Alaves 2-1, Dani Ceballos ne ya ci wa Real kwallayen.
Sai dai kuma abokin hamayyar Ronaldo wato Lionel Messi ya ci kwallo tara a gasar ta La Liga kuma, Barcelona tana ta daya a kan teburi bayan da ta ci wasa shida a jere.
Ronaldo ya ci kwallo uku a kakar bana a European Super Cup da Spanish Super Cup da wanda ya ci Apoel a gasar cin kofin Zakarun Turai.
Real Madrid za ta karbi bakuncin RCD Espanyol a wasan mako na bakwai a ranar 1 ga watan Oktoba, a kuma ranar ce Las Palmas za ta ziyarci.
Source: BBC Hausa
Title :
Ronaldo Ya Gagara Zura Kwallo Ko Daya A La Liga
Description : Cristiano Ronaldo bai fara wasannin cin kofin Spaniyar La Liga da kafar dama ba, yayin da har yanzu bai ci kwallo ba a gasar. Ronaldo bai b...
Rating :
5