Labarin da muke samu da dumi-dumin sa yanzu na nuni da cewa masana'antar Kannywood na shirin kamawa da wutar rikici babba bayan da alamu ke nuna cewa babban rikici ya barke a tsakanin jarumar nan da aka kora Rahma Sadau da kuma uban gidan ta watau Ali Nuhu.
Wannan rikicin dai ya far fitowa fili ne sakamakon yadda wasu manya jigogi kuma makusantan jarumi Ali Nuhu din suka fito a kafafen sada zumunta na manhajar Instagram suna aibata jaruma Rahma Sadau da munana kalamai da kuma zagi.
Shi dai Ali Nuhu tamkar wani bango ne a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood inda yake matsayin yaya ko kuma ma uba ga da yawa daga cikin jaruman fim din musamman ma mata.
Haka ma dai mun samu cewa Ali Nuhu din shine musabbanin shigowa da Rahma Sadau harkar fim kuma shine dalilin shaharar ta saboda sanya ta da yayi a cikin wasu fina-finan sa.
Source: Naij Hausa
Title :
Rikice Ya Barke Tsakanin Ali Nuhu Da Rahma Sadau
Description : Labarin da muke samu da dumi-dumin sa yanzu na nuni da cewa masana'antar Kannywood na shirin kamawa da wutar rikici babba bayan da alamu...
Rating :
5