Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa, INEC ta sa ranakun yi wa Sanata Dino Melaye na jihar Kogi ta Yamma kiranye.
Sakataren hukumar Augusta Ogakwu ne ya bayyana haka a ranar Litinin da yamma.
Idan ba a manta ba, an taba sa rana tun cikin watan Yuli da ya gabata, amma sai Melaye ya kai kara a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja.
Dino ya nemi a dakatar da kiranyen nasa. Sai dai kuma a makon da ya gabata alkalin kotun ya gatabar da shari’a, inda ya nuna cewa babu wani dalilin da zai sa a dakatar da kiranyen.
A cikin wasu hujjoji 12 da mai shari’a ya gabatar, ya kuma umarci hukumar zaben da ta ci gaba da kiranyen. Hakan ya sa INEC din ta fitar da sabon jadawalin kiranyen a jiya Litinin.
Sakataren hukumar dai ya ce sun aza rana ne bayan sun aika wa Melaye kwafen dalilan da suka sa ‘yan mazabar sa su ka gaji da wakilcin da ya ke yi musu, tare kuma da hadawa da sauran takardun da suka dace, domin ya je ya fara shirin kare kan sa.
RANAKUN KIRANYEN DINO MELAYE:
3. Ga Oktoba:
Za a fara tantance sunaye da sa hannun wadanda su ka nemi a yi kiranye.
5 Ga Oktoba:
Damka sunayen kungiyoyin sa-ido kan zabe.
9 Ga Oktoba:
Likawa ko buga sunayen daukacin masu so a yi wa Melaye kiranye.
11 Ga Oktoba:
Taron masu ruwa da tsaki a hedikwatar shiyyar da sanatan ke wakilta da Hukumar hedikwatar kananan hukumomin da ya ke wakilta.
12 Ga Oktoba:
Ajan na masu neman a yi kiranye da na Dino Melaye za su yi tantancewa.
12 Ga Oktoba:
Ranar tantancewa ta karshe.
Source: Premium Hausa
Title :
Ranakun Kiranyen Dino Melaye
Description : Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa, INEC ta sa ranakun yi wa Sanata Dino Melaye na jihar Kogi ta Yamma kiranye. Sakataren hukumar Augusta...
Rating :
5