Mesut Ozil na shirin kin yadda ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a Arsenal, bayan da dan kwallon ke son komawa Manchester United in ji jaridar Daily Mirror.
Sunday Express ta wallafa cewar Liverpool ta bukaci Barcelona da ta daina matsawa Philippe Coutinho a lokacin da ta yi kokarin sayen dan kwallo, inda Liverpool ta ki sayar da shi.
The Sun kuwa cewa ta yi Manchester City ta damu matuka cewar Paris St-Germain za ta bai wa Arsenal makudan kudi domin ta dauki Alexis Sanchez.
An shaidawa Manchester United ta biya fam miliyan 75 idan tana son daukar dan wasan Lazio, Sergej Milinkovic-Savic, itya ma Manchester City na son sayen dan kwallon in ji Daily Express.
Everton za ta taya dan wasan Arsenal Olivier Giroud a watan Janairun 2018, har ma ta tanadi fam miliyan 40 in ji Daily Mirror.
Daily Mail kuwa ta wallafa cewar ran Arsene Wenger ya baci matuka da ya sayar da Kieran Gibbs ga West Brom, fiye da barin Alex Oxlade-Chamberlain da ya koma Liverpool.
Source: BBC Hausa
Title :
Ozil Na shirin Komawa Man United
Description : Mesut Ozil na shirin kin yadda ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a Arsenal, bayan da dan kwallon ke son komawa Manchester United in j...
Rating :
5