Wata mawakiya 'yar Najeriya, Simi Ogunleye ta kafa tarihi, bayan ta shiga jerin mutanen da wakokinsu ke tashe a jadawalin wakokin da suka yi fice na Duniya a Amurka.
Da take zantawa da Sashen BBC Pidgin, Simi ta ce: "da ma na san za a rina, hakan kuma na nufin cewa kasuwata za ta bude kenan.
Ba zan taba sauya salon kidana ba, don kuwa shi ne mafarin duk wata daukaka da na samu yanzu."
Simi Ogunleye dai na gauraya Ingilishi da Yarbanci ne a cikin wakar tata mai taken 'Belle Sweet'.
Ta kuma yaba wa masu sha'awar wakokinta, don kuwa a cewarta "su ne suka kai ni duk matsayin da na samu kaina yau a cikinsa, su ne suka rika yayata kundin wakokinta, ba zan taba ba su kunya ba."
Simi na daya daga cikin fasihan mawakan Afirka da suka samu shiga sahun mawakan duniya, inda wakarta ta samu gurbi na biyar a fitattun wakokin da suke tashe cikin jerin Billboard Charts.
Shi ne kudin wakokinta na farko da ta sanya wa lakabin "Simisola".
Simisola ta fara waka ne da wakokin bege a coci, kafin ta shiga wasu wakokin a shekara ta 2014, lokacin da ta fitar da wakarta ta farko mai taken "Tiff and E no go funny."
Bayan wake-wake, Simi tana kuma harkar kade-kade.
Ana la'akari da adadin kwafen kundin waka nawa aka sayar cikin mako a fadin duniya, don sanya waka a jadawalin wakokin da suke tashe na Billboard Chart
Source: BBC Hausa
Title :
'Yar Nigeria Tashiga Jerin Mawaka Masu Tashe A London
Description : Wata mawakiya 'yar Najeriya, Simi Ogunleye ta kafa tarihi, bayan ta shiga jerin mutanen da wakokinsu ke tashe a jadawalin wakokin da suk...
Rating :
5