Ministan Ilimi Adamu Adamu, ya bayyana cewa kimanin mutane miliyan 65 zuwa 75 ba su iya karatu da rubutu ba a Najeriya, ya na mai cewa wannan abu kuwa babban tashin hankali ne matuka.
Ministan ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis, yayin da ya kai ziyara ga Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, a Birnin Kebbi.
Adamu ya je Jihar Kebbi ne domin halartar taron kwana biyu Ranar Karatu da Rubutu ta Duniya, wanda Hukumar Bayar da Ilimi ta shirya.
Ganin cewa yawan al’ummar Najeriya bai shige miliyan 170 ba, sai ministan ya ce adadin yawan wadanda ba su iya karatu da rubutu ba ya na da ban tsoro da nuna damuwa matuka.
“Ilimi shi ne ginshiki ko kashin-bayan ci gaban kowace kasa. Duk kasar da ba ta ilmantar da al’ummar ta, to babu shakka ta dauko hanyar durkushewa.”
Darakta a Hukumar Bayar da Ilimi na ‘Basic Education’, Jonathan Mbaka ne ya wakilci ministan. Ya ce gwamnatin
tarayya na kokarin kara inganta ilimi ta hanyar ilmantar da yaran da ba su samu damar karatu ba, su ke yawo a gari.
Adamu ya yaba wa uwargidan Gwamnan Kebbi, Aishatu Bagudu saboda kokarin ta wajen ilmantar da yara masu gararamba a gari, a jihar Kebbi, a karkashin shirin ta na ilmantar da almajirai da rage radadin talauci, wato MALPAI.
Source: Premium Hausa
Title :
'Yan Nigeria Miliyan 75 Basu Iya Karatu Da Rubutu ba-Hasashen Gwamnatin Tarayya
Description : Ministan Ilimi Adamu Adamu, ya bayyana cewa kimanin mutane miliyan 65 zuwa 75 ba su iya karatu da rubutu ba a Najeriya, ya na mai cewa wanna...
Rating :
5