Duk da matsalar da aka fuskanta a yammacin ranar Alhamis, kulob din Arsenal na da wasu abubuwa na bajinta da suke takama da su.........
Kulob din Arsenal ya doke kulob 57 daban-daban daga cikin wasa 64 da suka fafata da takwarorinsu, a shekarun da Arsene Wenger ya shafe yana jagorantar kungiyar.
Alexis Sanchez ya ci kwallo bakwai daga cikin wasansa takwas na karshe da ya buga wa Arsenal.
Hector Bellerin ya ci kwallonsa na farko a wasa 16 da ya buga wa Arsenal a gasar wasannin nahiyar Turai.
Sead Kolasinac ya taka rawar gani a kwallo hudu da aka ci, inda ya ci kwallo biyu ya kuma taimaka a kwallo biyu, daga cikin wasa biyar da ya buga wa Arsenal da suka hada da na Community Shield.
Kwallon da Kolasinac ya ci ita ce ta 200 da aka ci wa Arsenal a gida a gasar da ya buga a matakin nahiyar Turai, a karkashin jagorancin Wenger - inda suka ci kwallo 125 a Emirates, 69 a Highbury da kuma takwas a Wembley.
Source: BBC Hausa
Title :
Nataka Rawar Gani A Arsenal-Wenger
Description : Duk da matsalar da aka fuskanta a yammacin ranar Alhamis, kulob din Arsenal na da wasu abubuwa na bajinta da suke takama da su......... Kul...
Rating :
5