Mutane 19 su ka mutu sanadiyyar wani hadarin mota da ya faru a daidai Lambun Garban Bichi, kan hanyar Kano zuwa Katsina.
Kakakin Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa na jihar Kano, Kabir Daura ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN haka.
Hadarin inji Daura, ya ritsa da fasinjoji 34 wadanda ke cikin mitocin haya biyu, C20 bas da kuma Fijo J5, inda nan take mutane 18 su ka kone kurmus, yayin da na cikon 19 ya mutu a asibitin garin Bichi.
Ya ce sauran fasinjoji 15 kuma sun samu raunuka, kuma aka garzaya da su asibitin garin na Bichi.
Daura ya ce motocin biyu taho-mu-gamu su ka yi. Ya kuma danganta wannan hadari da gudun tsiya, gaggawa da kuma wuce mota a inda doka ta hana direba ya yi aron hannu ya wuce motar da ke gaban sa.
Source: Premium Hausa
Title :
Mutane 19 Sun Rasu A Hadarin Mota A Kano
Description : Mutane 19 su ka mutu sanadiyyar wani hadarin mota da ya faru a daidai Lambun Garban Bichi, kan hanyar Kano zuwa Katsina. Kakakin Hukumar Ki...
Rating :
5