Wata mummunar girgizar kasa ta faru a tsakiyar birnin Mexico, inda ta hallaka mutane kusan 150, yayin da dama suka jikkata, wasu kuma ta rutsa su a cikin buraguzan gine-gine da suka rushe.
Girgizar wadda ta kai karfin lamba 7.1 a ma'aunin girgizar kasa, ta rushe gomman gine-gine, a babban birnin kasar, Mexico City, wadanda suka hada da wata makaranta, inda ake ganin ta rutsa yara a ciki.
Tarin masu aikin sa-kai sun shiga taimaka wa masu aikin ceton gaggawa a kokarin da ake yi na gano masu rai a sassa daban-daban na birnin.
Bannar da girgizar ta haifar ba ta tsaya a babban birnin ba, har ma da wasu jihohi makwabta kamar Morelos da Puebla.
Wani rukunin gidaje mai hawa uku da wani babban kantin kayan masarufi da kuma wata ma'aikata na daga cikin gine-ginen da suka ruguje a babban birnin
Bala'in ya auku ne yayin da mutane da dama suka shiga wani atisaye na yadda ya kamata a yi a lokacin da girgizar kasa ta auku, daidai shekara 32 da ta wuce lokacin da wata girgizar ta hallaka dubban mutane.
Kasar ta Mexico na da matsalar aukuwar girgizar kasa, inda a farkon watan nan na satumba, wata mai karfin lamba 8.1, a yankin gabar kudu maso yammacin tekun kasar ta hallaka akalla mutane 90.
Source: BBC Hausa
Title :
Mummunan Girgizan Kasa Ya Hallaka Mutane Sama Da 130 A Mexico
Description : Wata mummunar girgizar kasa ta faru a tsakiyar birnin Mexico, inda ta hallaka mutane kusan 150, yayin da dama suka jikkata, wasu kuma ta rut...
Rating :
5