Yan kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra sun ce su ba 'yan ta'adda ba ne
Sun bayyana aka ne bayan da rundunar sojin kasar ta ayyana madugun kungiyar IPOB da magoya bayansa a matsayin 'yan ta'adda.
Wani dan uwan Kanu mai suna Prince Emmanuel Kanu ya shaida wa BBC ta wayar tarho cewa matakin da sojin suka dauka abin dariya ne.
"Wannan kalami abin dariya ne da ke fitowa daga dakarun soja saboda, na daya, ayyukan da muka kwashe shekara da shekaru sun nuna cewa IPOB kungiya ce mai tafiyar da al'amuranta lami lafiya.
"Mun yi ammana da abin da muke yi kuma muna yin sa yadda ya kamata bisa doka; ba ma kisa ba ma kuma sa wa wani ya yi kisa da yawunmu.
"Niyyarmu ba ita ce takalar yaki ba; niyyarmu ita ce mu fargar da kowa cewa muna cikin ukuba a Najeriya. Kuma irin yadda muke cikin wahala, haka mutane da dama ke cikin mawuyacin hali a arewacin Najeriya. Nnamdi Kanu yana yaki ne da zaluncin da ake yi wa 'yan Najeriya ba ka kawai kabilar Igbo ba".
Sai da mutane da dama na ganin wannan kalami ba shi da kanshin gaskiya musamman idan aka yi la'akari da yadda ake musgunawa wasu 'yan arewacin kasar da ke zaune a yankin kudu maso gabashin kasar.
Ranar Jumma'a ne dai daraktan watsa labarai na rundunar tsaron Najeriya Manjo Janar John Enenche ya aikewa manema labarai wata sanarwa, inda ya ce kungiyar, "ta sauya zuwa barazanar tsaro ga kasar".
Sanarwar ta kara da cewa, "Bayan mun yi nazari a tsanake kan abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan, muna son sanar da jama'a cewa ikirarin da mambobin IPOB ke yi cewa ita ba kungiyar tayar da hankali ba ce ba gaskiya ba ne. Don haka abubuwan da suke yi ta'addanci ne".
Ayyana wannan kungiya a matsayi ta 'yan ta'adda na nufin za a iya kama su sannan a garkame su.
Sai dai matsalar da hakan za ta iya janyowa ita ce ta yadda rundunar sojin ta gaza gane irin goyon bayan da IPOB ke da shi a kudu maso gabashin kasar.
Haka kuma ayyana su a matsayin 'yan ta'adda ka iya haifar da wata matsalar.Kazalika, sanya su a cikin jerin 'yan ta'adda na nufin dakarun sojin za su fuskanci kungiyoyin 'yan ta'adda uku wadanda suka hada da Boko Haram da tsagerun yankin Naija Delta da kuma su, ko da yake har yanzu rundunar ba ta iya murkushe ko wacce daga cikinsu ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Mu Ba 'Yan Ta'adda Bane-'Yan Biafara
Description : Yan kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra sun ce su ba 'yan ta'adda ba ne Sun bayyana aka ne bayan da rundunar sojin kasa...
Rating :
5