Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya shaida wa BBC cewa matasan kasar na cike da fushi shi ya sa ake samun kiraye-kiraye na raba kasar.
Cif Obasanjo ya ce "Matasa a kowanne yanki na Najeriya: gabas da yamma, kudu da arewa, suna cikin damuwa shi ya sa muke nema mafita ta kowacce hanya".
A cewarsa, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kokari a wurin yaki da cin hanci da rashawa da tabbatar da tsaro, ko da yake ba shi da kwarewa a fannin tattalin arziki.
Ya kara da cewa Shugaba Buhari ya tagaza sosai idan aka yi la'akari da yadda ya samu nasara a bangare biyu wadanda ya fi kwarewa a kai.
Chief Obasanjo ya ce Shugaba Buhari bai ba shi kunya ba saboda "al'amuran da muka san zai iya magancewa ya magance su."
Ya ce shugaban ya fara magance matsalar cin hanci da rashawa da kuma yaki da masu tayar da kayar-baya.
Ya ce: "Ba kowa ba ne zai gamsu da yadda yake yaki da cin hanci, amma abu muhimmi shi ne ya fara yaki da matsalar. Haka kuma mun san cewa a matsayinsa na tsohon soja zai yi iya kokarinsa wajen magance matsalar masu ta da kayar-baya."
Ya ci gaba da cewa ba zai taba yiwu ba a magance matsalar Boko Haram gaba daya, a lokaci daya, "saboda manyan abubuwan da suka jawo ta kamar talauci da rashin aikin yi da jahilci har yanzu suna nan, ba a magance su ba," kamar yadda ya ce.
An tambaye shi ko zai sake goyon bayan Shugaba Buhari idan ya sake tsayawa takara a zabe mai zuwa.
Sai ya ce: "Idan ya ce zai kara tsayawa takara zan duba aikin da ya yi duka, daga su ne zan yanke hukunci. Na zabe shi shekara biyu da ta wuce ne saboda zan iya zabar kowa amma fa ban da Goodluck Jonathan," a cewar Obasanjo.
Source: BBC Hausa
Title :
Matasan Nigeria Na Cike Da Fushi-Obasanjo
Description : Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya shaida wa BBC cewa matasan kasar na cike da fushi shi ya sa ake samun kiraye-kiraye na rab...
Rating :
5