Wata mata a Jamaica wadda aka ce ita ce mutum mafi tsufa a duniya, Violet Moss Brown ta rasu tana da shekara 117.
Fira ministan Jamaica ya sanar da labarin mutuwar dattijuwar a cikin wani sakon Twitter da ya wallafa.
"Mrs. Violet Mosse-Brown ta mutu, kuma ita ce mutum mafi tsufa a duniya. Shekarunta 117", inji Fira ministan.
Kafofin yada labarai a kasar sun ce matar ta mutu salin alin a wani asibiti da ke Montego Bay.
An haifi Violet Moss Brown wadda a farkon wannan shekara ne ta zamo mutum mafi tsufa a duniya cikin watan Maris na 1900.
Ta ce sirrin tsawon ranta shi ne cin komai, amma ban da naman alade da na kaza.
Haka zalika, danta Harold Fairweather, mai shekara 96 Violet ya ce gyatumarsa na son cin kifi da naman karamar dabba, a wani lokaci kuma takan ci naman kai.
Haka kuma tana son cin dankalin turawa da kayan marmari irinsu lemo da mangoro.
Haka zalika, ta ce ba ta shan giyar da aka yi ta da rake.
Ita ce dattijuwa mafi tsufa da aka taba tantancewa har kuma ta rike wannan kambu daga kasar Jamaica.
Mashahurin littafin tarihin duniya na Guinness Book of Records ne ya tabbatar da ita a matsayin mutum mafi tsufa a bana.
Source: BBC Hausa
Title :
Matan Datafi Tsufa Ta Fadi Sirrin Tsawon Rai
Description : Wata mata a Jamaica wadda aka ce ita ce mutum mafi tsufa a duniya, Violet Moss Brown ta rasu tana da shekara 117. Fira ministan Jamaica ya ...
Rating :
5