Masana kimiyya a Amurka sun kirkiro wani kwanjin hannu na mutum-mutumi mai na'ura wanda zai iya daga kayan da ke da nauyin da ya linka nauyinsa sau dubu.
Kirkirar wata gagarumar nasara ce a fasahar zayyana mutum-mutumi, kuma kamar yadda wakilin BBC Richard Hamilton ya bayyana, za a iya amfani da fasahar a fannoni da dama a nan gaba.
An kirkiro shi ne a Jami'ar Columbia da ke New York, a Amurka inda aka yi amfani da fasahar kirkira ta samfura, wato 3D Printer.
Masanan sun fara jarraba fasahar ne da wani dan kululun roba, wanda aka sanya kwayayen kumfar ruwan giya, daga nan kuma sai aka zaburad da wannan hannu ya kama aiki, ta hanyar amfani da wutar lantarkin da aka hada masa.
Daga nan sai aka gano cewa wannan hadi da aka yi ya sa wannan kwanji ko hannu zai iya budewa ya kuma tsuke daidai da yadda kwanjin hannun mutum yake yi, har ma ya zarta na mutum karfi sau 15.
Farfesa Hod Lipson, wanda ya yi kirkirar, ya ce wannan fasaha ta zama tamkar Ruwan Bagaja (ruwan baiwa na magance matsaloli daban-daban) ga masana kimiyya na wannan fanni.
Ya ce: ''Kafin yanzu, mun yi ta fama a wannan fanni, na yuwuwar yin mutum-mutumi, saboda muna ta yin mutum-mutumi da abubuwa masu karfi.
Idan ka duba yadda halittu suke, za ka ga dabbobi da dama, ba an yi su ne da wani abu mai karfi ba, an halicce su ne da 'yan tsokoki ko jijiyoyi marassa karfi, kuma saboda haka za su iya yin abubuwa da dama.
Saboda haka abu ne da zai ba da mamaki, idan ka duba irin abin da mutum-mutumin zai iya yi idan an yi shi da abu maras karfi.
Duka wadannan abubuwan daban-daban kenan zai iya yinsu.
Wani abu da zai zo a tunani shi ne yadda mutum-mutuminmu zai rika mu'amulla da mutane a zahiri.
Ba wai kawai mu'amulla a hoto ba, ko yin magana kadai, amma a ce ga shi yana taba mutane, misali a gidajen kula da jama'a - gidajen kula da yara da na kula da tsofaffi''
A baya dai masu bincike sun kirkiro mutum-mutumi iri daban-daban da ke ayyuka da dama, amma ba su iya gano yadda za su yi mai karfi ba sosai.
Farfesa Lipson ya yi amanna cewa da wannan nasara da suka samu ta kirkiro wannan hannu, shi da abokan aikinsa sun shawo kan daya daga cikin matsaloli na karshe na kirkiro mutum-mutumi mai aiki kamar mutum mai rai.
Source: BBC Hausa
Title :
Masana Sun Kirkiro Hanun Dayafi Na Mutum Karfi Sau 15
Description : Masana kimiyya a Amurka sun kirkiro wani kwanjin hannu na mutum-mutumi mai na'ura wanda zai iya daga kayan da ke da nauyin da ya linka n...
Rating :
5