Kungiyar Manchester United ta bayar da rahoton cewar ta ci ribar fam miliyan 581 a shekarar 2017, bayan da aka samu karin kudin kallon tamaula ta talabijin.
A shekarar ce United ta lashe kofin Europa League da League Cup, sannan ta saka hannu da kamfanoni 12 domin tallata masu hajjarsu da samun karin kudin kallon kwallo da na tallace-tallace.
Kungiyar ta karu da makudan kudin shiga da ya karu a kallon talabijin a kakar shekarar 2016-17, kakar farko daga shekara uku da aka shiga yarjejeniyar nuna wasa a talabibin mafi tsoka a tarihi.
A shekarar ce a ranar 30 ga watan Yuni kudin nuna wasan tamaula ya yi tashin gwauron zabi daga fam miliyan 194.1 zuwa fam miliyan 140.4, wato karin kaso 30 cikin dari kenan.
United tana mataki na daya a kan teburin Premier tare da Manchester City da maki iri daya da yawan kwallon da suka ci da wadanda aka zura musu.
Source: BBC Hausa
Title :
Man United Taci Ribar Fam Miliyan 581
Description : Kungiyar Manchester United ta bayar da rahoton cewar ta ci ribar fam miliyan 581 a shekarar 2017, bayan da aka samu karin kudin kallon tamau...
Rating :
5