Majalisar dokokin jihar Adamawa ta tsige wasu shugabannin majalisar su hudu.
Wadanda aka tsige kuwa sun hada da mataimakin shugaban majalisar Sunday Peter, shugaban masu rinjaje Musa Mahmud, mataimakin masu rinjaye Mutawali Mohammed da shugaban marasa rinjaye Justina Nkom.
Kamfanin dillancin labaran Najeria NAN ta ruwaito cewa kakakin majalisar Kabiru Mijinyawa ne ya jagoranci zaman tsige ‘yan majalisar a zaman majalisar bayan dawo daga hutun makonnin shida da tayi.
A zaman majalisar Abubakar Hayatu wanda ke wakiltan Uba da Gaya na jam’iyyar APC ne ya Karanto maganar tsigewa sannan Abubakar Abdurrahman da ke wakiltan kudancin Mubi na APC ya goyi bayan kudirin.
Majalisan ta zabi Emmanuel Tsamdu wanda ke wakiltan Madagali na jam’iyyar APC a matsayin mataimakin shugaban majalisan sannan Hassan Burguma wanda ke wakiltan Hong (APC) a matsayin shugaban masu rinjaye.
Abubakar Isa wanda ke wakiltan Shelleng daga APC ya zama sabon mataimakin shugaban masu rinjaye sannan Lamsumbani Dili shine sabon shugaban marasa rinjaye a majalisar.
Source: Premium Hausa
Title :
Majalisan Adaamawa Ta Tsige Shuwagabanninta Guda Hudu
Description : Majalisar dokokin jihar Adamawa ta tsige wasu shugabannin majalisar su hudu. Wadanda aka tsige kuwa sun hada da mataimakin shugaban majalis...
Rating :
5