Watanni kadan bayan tsohon dan takaran gwamnan jihar Kano Ibrahim Al-amin ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP daga APC, wani tsohon dan majalisar Wakilai Bala Baiko ya tattara nashi-i-nashi ya fice da ga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Ibrahim Baiko ya ce dukkan su ya’yan jam’iyyar ANPP da akayi maja tare aka kafa jam’iyyar APC an yi watsi da su. Ba a komai dasu a jam’iyyar.
Ya ce a lokacin zabe ne kawai aka bukace su amma bayan haka sai akayi watsi da su.
Yace Al-amin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun sha kokawa akan haka kafin Al-amin ya fice daga APC din.
Bala Baiko ya ce shi da wasu magoya bayan APC 20,000 ne suka canza sheka zuwa PDP domin su taimakawa jam’iyyar ta sami nasara a zaben 2019 a jihar da kasa baki daya.
“Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kammala shiri tsaf don komawa jam’iyyar PDP.” Inji Bala Baiko.
Source: Premium Hausa
Title :
Magoya Bayan Jam'iyar APC Dubu Ashirin Sun Koma PDP jihar Kano
Description : Watanni kadan bayan tsohon dan takaran gwamnan jihar Kano Ibrahim Al-amin ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP daga APC, wani tsohon dan majali...
Rating :
5